Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Wata Kwayar Sashin Jiki Da Zata Iya Warkar Da Kanjamau


Kwayoyin yakin cutar kanjamau
Kwayoyin yakin cutar kanjamau

Masanan kimiyya sun gano wata kwayar sashin jiki wadda suka ce zata iya shawo kan kamuwa da HIV, kwayar dake kawo kanjamau AIDS, daga yaduwa bayan ta shiga cikin jiki.

Masanan kimiyya sun gano wata kwayar sashin jiki wadda suka ce zata iya shawo kan kamuwa da HIV, kwayar dake kawo kanjamau AIDS, daga yaduwa bayan ta shiga cikin jiki.

A matakin bincike na farko da aka wallafa a mujjallar Nature, masu binciken sunce wannan sashin jikin, da ake kira MX2, ya nuna alamar yin aiki bisan yadda yake kauda HIV a jikin mutane, amfani da shi zai kai ga cigaban sabbin magunguna da warkarwa kan kwayar cutar.

Koda yake akwai sauran shekaru na bincike, Mike Malim, wanda ya jagoranci binciken a King’s College London, ya kwatanta abunda aka samu a matsayin ‘babban cigaba’ kuma ya kawowa masana fahimtar yadda kwayar HIV take yawo cikin jinin kariya na mutum.

Yace “har ya zuwa yanzu kadan muka sani kan wannan kwayar sashin jikin ta MX2, amma yanzu mun gane dukan yanayinta da kuma yadda take aiki a rayuwar HIV,”
Kimanin mutane miliyan 34 a dukan duniya suka kamu da HIV wanda ke kawo kanjamau – kusan yawancinsu a kasashe matalauta da masu cigaba.

Amma yayinda, yawanci a kasashe masu arziki, akwai magunguna masu inganci da yawa wanda ke kyale marasa lafiyar HIV suyi rayuwa na lokaci mai tsayi, suna da yawan sakamako mara kyau da kuma tsayayya ga maganin wanda ke zama damuwa idan anyi amfani da dashi na dogon lokaci.

A wannan bincike, Malim da kungiyar sa sunyi bincike akan kwayoyin jikin mutane a dakin bincike, wanda suka sa HIV cikin kwayoyi kala biyu – daya wanda MX2 ne yake aiki, da kuma dayan ba kome ciki – suka duba sakamakon duka biyun.
Binciken ya nuna cewa a kwayoyin da MX2 bashi da karfi, kwayar kanjamau ta yadu sosai, kuma a kwayar da aka sa ta aiki, HIV ya kasa yaduwa da zai kawo kwayoyin cutar.

Malim yace sakamakon ya nuna cewa MX2 shine jagoran wannan kiyayewar kwayar HIV cikin mutane, da kuma wannan sabun ilimin, akwai hanya biyu na kirkiro maganin wannan cutar ta wurin wannan sashin kwayar jikin.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG