An bayyana haka ne a wajen wanin taron manyan kungiyoyin da kuma wakilan shugabannin kiyaye kanjamau da aka yi a jihar Legos.
Wakilan Amurka a wajen taron sun kuma ziyarci wani asibiti dake tsibirin jihar Legos domin su ga kokarin da ake yi na kawarda yaduwar wannan kwayar cutar, da kuma manufar cinma burin hana yaduwar cutar baki daya da kuma shawo kan nunawa masu fama da cutar banbanci. Haka kuma ana kokarin ganin cutar ta daina kashe mutane baki daya.
Bukin ya sami hallatar masanan magani, da masu maganin gargajiya masu aiki tsakanin mutane dake dauke da kwayar cutar.
Shugaban wakilan cibiyoyin Amurka USAID/PEPFAR, Mr. David Stanton, ya kara bayyana bukatar daukar matakin hana yada cutar daga uwa zuwa jariri, yace wannan ita ce muhimmiyar hanyar maganin yada cutar. Ya kuma tabbatarwa kungiyoyin cigaban hadin kan mutanen Amurka na yaki da kwayar cutar.
PEPFAR wata kungiya ce da ta bada tallafin dalai biliyan goma sha biyar domin yaki da cutar kanjamau na tsawon shekaru biyar daga 2003 zuwa 2008 karkashin tsohon shugaban Amurka, George W. Bush, domin yakin da cutar kanjamau.