An sace yaran ne bayan da wasu da ake zargin mayakan kabilar Murle ne su ka kai hare-hare kan wasu kyauyuka a yankin Gambella da ke kudu maso yammacin Sudan ranar Jumma'a. An hallaka mutane sama da 200 a hare-haren.
Gwamnatin Sudan Ta Kudu ta ce ta na bada sojojin Habasha din hadin kai. Mukaddashin Ministan Harkokin Waje Peter Bashin Gbandi ya ce babu hannun sojojin gwamnatin Sudan Ta Kudu a hare-haren na ranar Jumma'a.
Baba Medan, gwamnan jahar Boma inda 'yan kabilar ta Murle ke da zama, ya dora laifi kan mayakan bangaren 'Cobra,' wadanda tsoffin 'yan tawaye ne na yankin.
To sai dai jagoran 'yan tawayen na Cobra, David Yau Yau, ya ce sam ba su ba ne. Ya ce wasu 'yan tawayen da shi kansa Medan ya ba su makamai ne su ka aikata.