Kwamandan runduna ta 7 ta mayakan ruwan Amurka, Vice Admiral Joseph Aucoin, ya fadawa ‘yan jarida yau lahadi cewa an kawo karshen aikin neman may6akan da suka bata. A fakaice dai, hukumomin Amurka suna nuna cewa babu wanda ya tsira da rai daga cikin mayakan bakwai, koda yake Vice Admiral Aucoin ya ki yace ko gawarwaki nawa aka gano har sai bayan an sanar da iyalan mamatan.
Aucoin yace ruwan teku ya shiga ya mamaye dakunan kwana a jirgin, kuma bangaren hannun daman a jirgin ya lotsa ciki.
Yace jikrgin ruwan yakin ya lalace sosai.
Yace da yawa daga cikin mayakan dake aiki a wannan jirgin ruwa suna barci a lokacin da ya ci karo da wani jirgin ruwan daukar kaya mai dauke da tutar Philippines mai suna ACX Crystal. Yace za a iya gyara jirgin ruwan yakin na USS Fitzgerald, amma zai dauki watanni.
Har yanzu babu wani bayani na yadda aka yi har jiragen ruwan guda biyu suka kara da junansu.
Facebook Forum