An bayyana jerin ma'aikatun sabbin ministocin shugaba Buhari na Najeria, inda yawanci tsoffin ministocinsa su ka koma tsoffin ma'aikatunsu.
Kama daga ministan Abuja Musa Bello, Hadi Sirika na jiragen sama da Abubakar Malami na shari'a duk sun koma ma'aikatunsu na da.
Sai dai Hadi Sirika ya ce a wannan karon zai kawo kamfanonin jirage da kuma jinginar da filayen jirgi.
Shi kuwa Osagie Ehanire, wanda a baya karamin ministan lafiya ne, yanzu ya zama babban minista don rashin dawowar Isaac Adewole.
An rage wa Babatunde Fashola ma'aikatar lantarki daga jerin ma'aikatun sa 3 da su ka hada da na ayyuka da gidaje.
Sabbin ministoci sun maye gurbin wasu da ba su dawo ba, da su ka hada da Pauline Tallen a ma'aikatar mata da ta zauna ba minista tun murabus din Jummai Alhassan, sai dai tana karkashin kulawar tsohuwar karamar ministar kasuwanci da masana'antu Aisha Abubakar, Sunday Dare a ma'aikatar matasa da wasanni, inda a baya Solomon Dalung ya ke matsayin babban minista.
Sabuwar minista Sadiya Umar Faruk ta samu wata sabuwar ma'aikata ta ayyukan jinkai yayin da shugaban kungiyar masu marawa Buhari baya BSO, Dr. Mahmud Muhammed ya ke ma'aikatar muhalli.
Isa Ali Pantami ya samu ma'aikatar sadarwa. Ya ce idan ya riski bayanin shugaba Buhari bai ce zai fitar da mutane daga talauci ba amma zai iya bakin kokarinsa, don Allah ke iya fitar da mutane daga talauci.
Ma'aikatar lantarki da aka yage daga kulawar Fashola yanzu ta shiga hannun sabon minista Injiniya Sale Mamman.
Manjo Janar Bashir Magashi daga Kano ya zama ministan tsaro inda a baya Burgediya Janar Mansur Dan Ali ya ke.
Har yanzu dai shugaba Buhari bai sauya ma'aikata daga matsayinsa na ministan fetur ba, inda tsohon gwamnan Bayelsa Timipre Silva ya ke matsayin karamin minista.
Saurari Cikakken rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya daga Abuja:
Facebook Forum