Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce sanadiyar mutuwar mutane 44 a Libya zai iya zama laifin yaki.
A ta bakin jami’an, barin wutar da aka yi a daren Talatar da ta gabata, a babban birnin kasar ta Libya wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 44, wasu rahotannin ma na cewa mutane 55 ne suka mutu, sama da mutane 130 kuma suka ji rauni, hakan na iya zama laifin yaki.
A wajen wata cibiyar tsare mutane, a babban birnin Tripoli, jiya Laraba, wadanda suka tsira da ransu, sun ga yadda masu bincike, suke tona barguzan gine-ginen, da suka fadi, bayan sun kwashe lokaci mai tsawo, a waje ba tare da abinci ko ruwan sha ba.
“Mu zaman lafiya kawai muke so” a cewar wata mata “'yar Somaliya, wadda ta fake a karkashin wata bishiya, yayin da jami’ai ke neman gawarwaki har zuwa rana. Matar ta kuma ce, “daga Somaliya muka je Yemen, daga nan muka je Sudan, sannan muka zo nan. Nan din ma, ba bambanci da Somaliya”.
A wani dakin ajiye gawarwaki, dake birnin Tripoli, an nannnade gawarwaki, don a gudanar da bincike na musamman akan su, a yayinda wadanda suka ji rauni a asibitin, kuma ake yi masu jinya, wasu ma basa cikin hayyacin su.
Facebook Forum