Wannan Kudurin, idan ya samu karbuwa har ya zama doka, zai bada damar hana shigowa da Janareta, bayan haka duk wanda ya karya dokar zai fuskanci hukuncin dauri har tsawon shekara goma.
Sanata Mohammed Birma Enagi, mai wakiltar jihar Naija ta Kudu a majalisar dattawan Najeriya karkashin jam'iyyar APC, ya ce tabarbarewar harkar wutar lantarki a kasar, da ta ki ci ta ki cinyewa tare da kuma irin rawar da ‘yan kasuwa ke takawa wajen illata yanayi, da irin janaretan da suke shigowa da su kasar, sune suka sa shi ya kawo wannan kudurin, domin a magance wadannan illolin, sannan a tsaftace harkar wutar lantarki a kasar.
Daya daga cikin 'yan kwamitin kula da harkar wutar lantarki, Sanata Ahmed Babba Kaita, ya ce yana goyon bayan wanan kuduri domin zai hana illata yanayi kuma zai sa a tashi tsaye wajen magance matsalar wuta a kasar.
Amma shugaban kwamitin kula da wutar lantarki a majalisar wakilai, Aliyu Magaji Da'u, ya ce an bar jaki ne ana dukan taiki, saboda ba janareto ne matsalar Najeriya a yanzu ba, matsalar tana wurin shugabanni domin in har aka maida hankali wajen samar da wutar lantarki, babu wanda zai ma kalli janareto balle har ya saya ya sa a gidan sa.
Amma ga mai ba Ministan Wutar Lantarki shawara akan batun wutar lantarkin tsibirin Mambila, Idris Mohammed Madakin Jen, ya ce dokar tana da kyau domin ta haka ne kadai zai a yi maza-maza a kammala Mambila saboda wuta ta samu a kasa.
Amma ga Isa Sanusi, dan kasa dake zaune a birnin tarrayya Abuja, wannan batu na hana shigowa da janareto shine yunkuri mara ma'ana da aka taba yi a majalisar kasar tun da aka kafa ta, kuma ya ce mutane suna iya mutuwa idan babu janareta saboda babu wutar lantarki a kasar.
Rashin wutar lantarki na daga cikin kalubalen da Najeriya ke fuskanta tsawon shekaru masu yawan gaske.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti.
Facebook Forum