Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Dawo Da Kayayyakin Tarihin Masarauta Benin Da Aka Sace Sama da Karni Guda


An dawo da wasu tagulla biyu na Benin zuwa fadar gargiya a Najeriya ranar Asabar din da ta gabata, sama da karni daya bayan da sojojin kasar Birtaniya suka yi awon gaba da su, lamarin da ya kara sanya fatan za a iya mayar da wasu dubban kayayyakin tarihi zuwa kasashen asalin da aka sace su.

Masu bincike da masu mulkin mallaka da galibi a kasashen Turai ne suka sace kayayyakin tarihin, cikin muhimman kayayyakin tarihi na Afirka daga Masarautar Benin, wanda a yau aka fi sani a matsayayin kudu maso yammacin Najeriya. An kera kayayyakin tarihin ne tun daga karni na 16, a cewar gidan tarihi na Biritaniya.

A wani gagarumin biki na dawo da kayayyakin tarihi da suka hada da kan wani shugaba ko sarki, mai magana da yawun fadar Oba da ke birnin Benin, Charles Edosonmwan ya bayyana cewa an yi awon gaba da wasu daga cikin tagulla har zuwa kasashen New Zealand, Amurka da Japan.

Jami’ar Aberdeen da Kwalejin Jesus ta Jami’ar Cambridge ta mika kayayyakin tarihin biyu ga babbar hukumar Najeriya a watan Oktoba, amma har yanzu ba su koma jihohin asalinsu ba.

Komawar wani muhimmin mataki ne a cikin shekaru da dama da kasashen Afirka ke ta kokarin kwato kayayyakin da aka wawashe a lokacin mulkin mallaka.

Masana tarihin fasahar Faransa sun ce kimanin kashi 90% na kayayyakin tarihin Afirka suna Turai. Musée du quai Branly–Jacques Chirac a birnin Paris kadai yana rike da kayayyakin tarihi kusan 70,000 na Afirka kuma dubun dubatar wasu na gidan tarihin Ingila.

- REUTERS

XS
SM
MD
LG