Kakakin rundunar Kaftein Salisu Mustapha ya bada tabbacin cewa yadda aka yi kirsimatin bara lami lafiya da yadda Allah ma haka za'a yi bana. Ya ce a wuraren ibada wato mijami'u da wuraren shakatawa idan an fito daga mijami'un za'a saka jami'an tsaro. Ban da haka wuraren da suka san an fi samun tashin hankali za'a kara jami'an tsaro domin haka ya bukaci jama'a su yi hakuri. Shigowa da fita birnin Jos za'a dinga yin binciken kwakwaf ma duk ababen hawa. Wadannan matakan za'a yi anfani da su daga yanzu har zuwa sabuwar shekara.
Dangane da fashi da makami da ake yawan yi a hanyoyin Dangi zuwa su Kanke da Amper ya ce tun da yanzu sun gane inda ake aika ta'asar zasu zaunar da sojoji a wurin na din-din-din. Shi ma kwamandan Civil Defense Vincent Bature ya ce jami'ansu sun hada kai da wasu jami'an tsaro domin tabbatar da zaman lafiya tsakanin al'umma.
Kwamishanan yada labarai na jihar Filato Yiljap Abraham ya kira mutanen jihar su nemi zaman lafiya mai dorewa.Ya ce basa son mutane su kasance cikin tsoro suna aiki da jita-jita cewa wasu zasu kawo hari ko wani abu. Ya roki mutane su hada kai da jami'an tsaro su kuma yi biyayya da abun da aka fada masu. Su guji abun da zai kai ga tada hankali a mayarda hannun agogo baya. Ya ce ashirye suke su cigaba da daukan kwararrun matakan tsaro domin inganta zaman lafiyan da aka samu yanzu.
Mai bishara Musa Paul Gindiri huduba ya yiwa kirista da mazauna jihar. Ya ce duk mai bin Yesu da gasken gaske to dole ya nuna halin kauna da halin gafartawa da halin taimako. Wadannan su ne halayan da ya kamata su kasance da duk mai bin Yesu. Masu hannu da shuni su tuna da wadanda basu da shi. A wannan lokacin ya kamata a tuna da marasa karfi.
Zainab Babaji nada karin bayani.