An lalata kayan gwamnati sakamakon zanga zangar da daliban makarantun sakandare suka yi a kwanakin baya.
Gwamna Ajimobi ya yi furucin ne a lokacin da yake tattaunawa da wani radiyo mai zaman kansa a Ibadan fadar gwamnatin jihar. Gwamnan yace ba zata yiwu ba mutane su lalata kayan gwamnati, su ki biya, kana su ki neman gafara game da ta'asar da suka tafka.
Gwamna Ajimobi yace su ba zasu amince da tada zaune tsaye ba a jihar. Da ya juya kan bukatun 'yan kwadagon na a biyasu albashi da alawus alawus da suke bin gwamnati, sai ya ce ahalin yanzu basu da isassun kudi kuma basu kadai ba ne ke bin gwamnatin bashi. Yace akwai 'yan siyasa amma basu shiga yajin aiki ba.
Mr. Ajimobi yace yajin aikin 'yan kwadagon bai yi tasiri ba. Yace sun kira yajin aiki amma kananan ma'aikata ne suka shiga yajin aikin. Manyan ma'aikata suna aiki kuma kome na tafiya daidai. Yace ya mika sunayen sabbin kwamishanoni don majalisa ta tantancesu. Kafin mako mai zuwa zasu fara aiki don jihar ta cigaba. Saboda haka yace yajin aikin tamkar aikin banza ne harara a duhu.
Ga karin bayani.