A cewar rahoton da Stacey Knott ta hada daga birnin Accra, bayan da Pelosi, wacce ita ce Shugabar Majalisar Wakilan Amurka ta farko mace, ta iso Ghana ranar Lahadi da tawagar wacce ta hada da ‘yan kungiyar majalisar dokokin tarayyar Amurka Bakaken Fata, da ita da sauran ‘yan Majalisar dokokin tarayyar Amurka sun ziyarci Elmina Castleand inda su ka dubi kofar bayin da ake ma lakabi da mashigar da ba a dawowa da ke ginin zangon bayi da ake kira Cape Coast Castle da Turance, inda duka biyun wuraren jibge bayi ne, gabanin jigilarsu daure da sarkoki a jirgin ruwa zuwa wasu kasashe.
Pelosi, wacce ta zauna ganga da Mike Oquaye, Kakakin Majalisar Wakilian Ghana, ita ce shugabar Majalisar Amurka ta farko da ta yi da ta yi jawabi ga majalisar wakilan Ghana. Ta gaya ma ‘yan Majalisar Ghana cewa musabbabin ziyararta da tawagarta shi ne amsa cewa abin da ya faru a baya ya faru, tare kuma da hangen gaba.
Ta ce "tawagarmu ta saduda da abubuwan da ta gani a wannan satin. A rukunin ginin Elmina, mun ga wurin dakunan bayi, inda aka yi ta gana azabar rashin imani ga dubban bayi. A rukunin ginin Cape Coast Castle, mun tsaya gaban mashigar da ba a dawowa, inda miliyoyin mutane su ka yi bankwana ta karshe da Afirka gabanin a yi jigilarsu zuwa rayuwar bauta. Zuwan mu nan ya yi matukar canza tunanin kowannenmu -kai, ko da ma ka taba zuwa nan.”
Facebook Forum