A jawabin daya gabatar wajen bude taron shugabanin hukumomin Leken asiri a Anuja daraktan hukumar leken asiri na rundunar sojojin Amurka Rear Admiral Trem Wilbot, ya ce yana da kyau su duba mahimmancin taron da mahimmancin aiki tare yayinda suke aikin samar da zaman lafiya.
Admiral Wilbot yace abubuwa uku ne rundunar sojojin Amurka ta sa a gaba yayinda duk wata arangama ta taso. Na farko zasu so su san wuraren da suka samu kansu ciki. Na biyu zasu yi kokari su gama da abokan gaba kana su karfafa matakan tattara bayanan sirri
Taron ya hada shugabanin hukumomin leken asirin na sojojin kasashen yakin tapkin Chadi da na sojojin Amurka dake nahiyar Afirka da ake cewa AFRICOM a takaice da kuma wasu hafsoshin sojojin kasar Faransa.
Babban daraktan leken asiri na rundunar sojojin Najeriya Air Vice Marshal Muhammad Sani Usman ya jaddada aikin kawar da ‘yan ta’adda a duk kasashe. Yace ba zasu amince da ta’addanci musamman na kungiyar ISIS da al-Qaida da ma abokansu da suke haddasa barazana ga zaman lafiya a duniya musamman a wannan yankin ba. Saboda haka yace dole su fahimci cewa babban abun da suka sa a gaba shi ne kakkabe duk wani nau’in ta’addanci na ‘yan ta’adda domin muddin aka bari ya samu gindin zama a kasa daya, hakika yana iya mamaye duk yankin.
Kanar Mejo Lamin daraktan leken asiri na rundunar Jamhuriyar Nijar y ace taron da su keyi na neman hada gwuiwa ne domin su samu damar kawar da matsalar ‘yan ta’adda domin jama’arsu su samu zaman lafiya da walwala.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani
Facebook Forum