Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Bude Kasuwar Baje Kolin Bana A Jihar Plato


Kimanin kasashe takwas, da suka hada da Pakistan, da Indiya, da Masar, da Sudan, da Ghana, da Nijar da sauransu suka halarci kasuwar baje kolin ta bana a jihar Plato.

Gwamnatin jihar Plato ta yi alkwarin ba duk wani mai bukatar gudanar da kasuwanci a jihar yanayi mai kyau da zai bunkasa kasuwancin sa don cigaban jihar da kasa baki daya.

Mataimakin gwanan jihar Plato, farfesa Sonni Tyoden ne ya bayyana haka yayinda yake bude kasuwar baje kolin bana a Jos, fadar jihar Plato.

A cewar farfesa Sonni Tyoden, jihar Plato na da yanayi mai kyau da amfanin gona iri iri, da ma'adinai, da wuraren yawon bude ido da dama da kasashen duniya zasu amfana da su.

Mataimakin gwamnan ya ce jihar ta fadada bangaren ma'adinai, ta kuma rattaba hannu a wata yarjejeniya da masu zuba jari daga kasar China don gudanar da aikin ma'adina a jihar.

Shugaban cibiyar kasuwanci, ma'adinai, da masana'antu da harkokin aikin gona a jihar Plato, Bulus Daren, ya ce kasuwanci na kan gaba wajen habbaka tattalin arzikin kasa. Ya kuma ce idan al'ummar jihar ta hada kai, rayuwa zata zama da sauki.

Shugaban shirin kasuwar baje kolin Mr. Simon Tangni, ya ce kasuwar baje kolin wani zarafi ne da matasa da dama zasu sami ayyukan yi don rage zaman kashe wando. Ya kara da cewa, rashin aikin yi na daya daga cikin abubuwan da suka kawo rashin zaman lafiya a jihar.

Hajiya Hauwa Soda, da ta zo daga kasar Sudan ta yaba da yanayin kasuwar ganin yadda jama'a ke cudanya ba tare da nuna wani bambancin addini ba.

Shi kuma evangelist Musa Paul Gindiri, shugaban kungiyar mahakan ma'adinan jihar Plato ya ce yanzu an fara gane muhimmancin hakar ma'adinai da alfanun su ga tattalin arzikin jihar da ma kasar baki daya.

Wani Shugaban al'umma Alhaji Yusuf Sarumi, ya jaddada batun zaman lafiya don samun cigaba a Najeriya, ya ce don zaman lafiya shine kasuwanci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00

Facebook Forum

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG