Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An bada belin Hamma Ahmadou shugaban hamayyar Nijar


Hamma Ahmadou,shugaban hamayyar jamhuriyar Nijar
Hamma Ahmadou,shugaban hamayyar jamhuriyar Nijar

An bada belin Hamma Amadou shugaban hamayyar jamhuriyar Nijar jiya Talata, bayan tsareshi na tsawon watanni biyar bisa zargin safarar jarirai, zargin da yace bita da kullin siyasa ne.

Makon da ya gabata, Amadou ya sha kaye a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da shugaba Mahamadou Issoufou ya lashe, domin wa’adin mulki na biyu, da kashi casa’in da biyu cikin dari na kuri’in. Jam’iyun hamayya sun kauracewa zaben. Abinda yasa jam’iya mai mulki ta sami gagarumar nasara ke nan.

Wani kakakin jam’iyar hamayya yace, zargin kage ne da aka yi amfani da shi aka kama Amadou domin hana shi yin tasiri a zaben.

Kakakin jam’iyyarsa Ousseini Salatou yace, an kulle Hama Amadou aka hana shi yakin neman zabe. Ya yi fama da rashin lafiya a lokacin yakin neman zaben kafin a tafi da shi jinya a kasar Faransa kwana hudu gabanin zaben zagaye na biyu.

An kama kusoshin jam’iyun hamayya da dama tun daga watan Yuni shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, bayanda ‘yan sanda suka kaddamar da bincike kan zargin safarar jarirai daga Najeariya da iyalan attajirai suke yi a Nijar. Matar Amadou na daga cikin wadanda aka kama, kafin daga baya aka sake ta.

Ranar Asabar za’a rantsar da shugaba Mohammadu Issofou domin wa’adin mulki na biyu na shekaru biyar.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG