Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China ta Zargi Wani Babban Jami'in Soji da Laifin Cin Hanci


 Guo Boxiong babban jami'in soji da aka kora daga kwamitin zartaswar jam'iyyar kwaminisanci mai mulkin kasar.
Guo Boxiong babban jami'in soji da aka kora daga kwamitin zartaswar jam'iyyar kwaminisanci mai mulkin kasar.

Shugaba Xi Jinping ya kori Guo Boxiong babban jami'in soji kuma dan majalisar zartaswar jam'iyyar kwaminisanci dake mulkin kasar.

Shugaban kasar Sin Xi Jinping mai yakar cin hanci da rashawa ya kori wani babban jami'in sojoji daga kwamitin zartaswar jam'iyyar kwaminisanci mai mulkin kasar.

Guo Boxiong dan shekara 73 da haihuwa daya cikin manyan jami'an sojojin kasar ana zarginsa da karban na goro kafin a karawa sojoji girma. An cireshi daga jam'iyyar jiya Alhamis kana aka mikashi ga mahukntan sojojin kasar.

A watan Maris aka soma binciken dansa Guo Zhenggang akan zargin aikata laifuka da ba'a bayyana ba kafin a kawo kan shi Guo Boxiong a watan Afirilu

An jima ana zaton hakan zata faru kamar yadda aka saba gani yana faruwa a kasar

Guo Boxing zai gurfana gaban kotun dake karkashin ikon jam'iyyar kwaminisanci lamarin da ya sa ana kyautata zato za'a sameshi da laifi a kuma daureshi

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG