Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: Yadda Zanga-Zanga Gaban Fadar Shugaban Kasa Ta Koma Tarzoma


Daruruwan mutane ne suka fito gaban fadar ta White House rike da kwalaye a hannayensu domin kalubalantar mutuwar Mr Floyd, da kuma dangantakar da ke tsakanin ‘yan sanda a Amurka da mutane, musamman ma bakaken fata.

Masu zanga-zangar dai sun fito ne tun da safiyar ranar Lahadi suka zagaye fadar Shugaban Kasar, inda suka ta yin arangama da ‘yan sanda, har ma da jifansu da kwalaben ruwa domin nuna bacin ransu.

A nasu bangaren, su ma ‘yan sandan sun yi ta jefa ababen fashewa da barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu boren.

Daga baya lamarin ya kara muni, inda har ta kai ga kone-kone, dalilin da ya sa magajiyar garin birnin Muriel Bowser ta ayyana dokar zama a gida a daren na jiya.

Mr Floyd dai ya mutu ne bayan da ‘yan sanda suka zarge shi da aikata wani laifi.

Wani hoton bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta da na yada labarai, ya nuna yadda wani dan sandan ya danne Floyd a wuya da gwiwarsa – lamarin da ake zargin ya yi sanadiyyar mutuwarsa.

Wani lamari mai ban mamaki dangane da wannan zanga zanga shi ne, yadda yawancin wadanda suka fito gudanar da zanga-zangar suka kasance fararen fata.

Dukkaninsu wato sun fito ne domin su hada kai da juna, a kwato wa Amurkawa bakaken fata ‘yancinsu.

Tsabar yadda gaban gidan shugaban ya cika, sai da aka jibge wasu Karin jami’ai na musamman kan saman ginin gidan, baya ga daruruwan ‘yan sandan da suka zagaye mutane a kan tituna domin su sanya ido kan masu zanga zangar.

An jima dai ana zargin ‘yan sandan Amurka da nuna wariyar launin fata, musamman idan ya shafi bakaken fata – zargin da jami’an tsaron suke musantawa.

A karshen makon da ya gabata, tarzomar da aka yi ta fama da ita a Washington DC din dai ta janyo jikkata wasu jami’an tsaro masu farin kaya fiye da 60, an kuma kama masu zanga zanga su fiye da ashirin.

Kana, an kara tura dubban jami’an tsaro cikin jihohi da dama, har da nan Washington DC, domin su taimakawa ‘yan sanda a yayin zanga-zangar.

Duk wannan dai na faruwa ne yayin da kasar ta amurca ke ci gaba da zama kan gaba a duk fadin duniya wajen yawan masu coronavirus, da kusan mutum miliyan 2, amma hakan bai hana mutane fitowa wajen cunkoso ba domin gudanar da zanga zangar tasu ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG