Wanda ministan tsaron kasar Rashan ya gabatar da hujjan hakan kuma ya soki lamirin jami’an kasar Turkiyyar ciki ko harda shugaba Racep Tayip Erdowan da iyalansa.
Mai Magana da yawun ma’aikatar wajen Amurka Mark Toner ya fada jiya Laraba cewa ba kanshin gaskiya cikin wannan batu cewa wai gwamnatin Turkiyya na sayen mai daga kungiyar ISIS, yace wannan zuki ta mallaki ne ba kanshin gaskiya ko kadan.
Shiko mai magana da yawun Fadar White House Josh Earnest cewa yayi idan da gaske kasar ta Rasha take yi to su tinkari shugaban kasar Syria Bashar Al-Assad da wannan batun.
A satin da ya shige ne gwamnatin Amurka ta soki gwamnatin Syria da sayen mai daga hamnnun kungiyar ISIS abinda yasa ta kakaba mata takunkunmi