Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Tayi Tur da Harin da ISIS Ta Kai Baghdaza A Iraqi


Wurin da aka kai hari a Baghdaza jiya Lahadi
Wurin da aka kai hari a Baghdaza jiya Lahadi

Amurka ta yi Allah wadai da harin ta'adancin da kungiyar ISIS ta kai a Bagadaza, wanda ya halaka akalla mutane 124, da jikkata 186, jiya Lahadi.

A cikin sanarwa da kakakin majalisar tsaron Amurka Ned Price ya bayar yace "Muna ci gaba da hada kai da mutane da gwamnatin Iraqi, a yunkurin da muke yi baki daya na ganin bayan ISIL. Wadannan hare hare suna kara karfafa kudurinmu na ci gaba da bada goyon baya ga hukumomin tsaron Iraqi, yayinda suke ci gaba da kwato yankunan kasar daga hanun ISIL, a kuma dai dai lokacinda muke ci gaba da matsa kaimin yanke jijiyoyin kungiyar ta'addancin da shugabanninta."

Harin ta'adanci a Baghdaza
Harin ta'adanci a Baghdaza

Tunda farko a jiya Lahadi, ministan tsaron kasar Khalid al-Obeid, ya gana da jakadan Amurka a Iraqi Stuart Jones, a Bagadaza. Jami'an biyu sun tattauna kan yadda zasu kara hada kai wajen yaki da ISIS.

An kai harin ne da wata babbar mota da aka dankarawa nakiyoyi a wani wurin da ake hada hada. Harin ya kashe akalla mutane 119, ya jikkata 170. Wannan shine hari mafi muni da aka kai a babban birnin kasar a bana.

Kungiyar ta ISIS ta dauki alhakin kai harin da ta kai a gundumar da ake kira Karrada. Kungiyar tace tana auna 'yan shi'a ne.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG