Wani dan kunar bakin waken kungiyar ta’addancin Taliban ya kutsa da wata babbar motar kunar bakin cikin wata tawagar ‘yan sanda a Kabul babban birnin kasar Afghanistan.
Inda jami’an tsaro akalla 30 suka mutu aka raunata da dama daga cikinsu. Jami’an gwamnatin Afghanistan sun ce an sami tashin bama-baman ne daya bayan daya.
Sannan shedun gani da ido sun fadawa muryar Amurka cewa sun ga ‘yan sanda na kwashe gawarwakin wadanda suka mutu da kuma dimbin wadanda suka ji rauni sakamakon tashin bama-baman.
Shugaba Ashraf Ghani yayi Allah wadai da harin, da cewa wannan wani hari ne na cin zarafin bil’adama. Ya kuma umarci ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar da ta gudanar da binciken yadda aka shirya tafiyar jerin gwanon motocin ‘yan sandan.
Tare da alkawarin daukar matakin ladabtarwa matukar aka sami sakaci a lamarin harin da ya hallaka tare da jikkata jami’an tsaron da ke kan hanyar zuwa Kabul daga tsakiyar gabashin lardin Wardak a shirye-shiryen karamar sallah. Tuni ‘yan Taliban din suka dauki alhakin kai harin.