Wannan zaben shine ya kawo tsohon Firayim Minista Roch Marcri Christian Kabore a matsayin sabon shugaban kasar.
Fadar White House a cikin wata sanarwa ta yaba wa ‘yan kasar na ganin sun kare demokaradiyya abinda Amurka tace tana fata taci gaba da hulda da ita musammam na ganin yadda tayi anfani da wannan damar domin sake hada kan kasar tare da bunkasa ayyukan ci gaba.
Tun a ranar Talata ne dai shugaba Kabore ya godewa dinbin magoya bayan sa yace zai dukufa ne wajen yiwa kasa aiki bada bata lokaci ba.
Yace ya danganta wannan nasarar tasa ce ga ‘yan kasar wadanda suka rasa rayukan su domin borin da suka yi na korar shugaba Blaise Campore.
Kabore tsohon na hannun damar Campore yayi nasarar zaben ne na ranar Lahadin data gabata da kashi 53 na daukacin kuriun da aka jefa, wanda wannan yasa ya zama sabon shugaban kasar dake Africa ta Yamma sabo fil zababbe.
Sai dai kawo yanzu ba a riga an fidda sakamakon zaben’ yan majilisar dokokin kasar ba tukunna.
Mutane miliyan 5 ne da farko akayi wa rajistan jefa kuria, wanda yan takara 14 ne suka tsaya takarar mukamin shugaban kasa.