Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka ta saka Koriya ta Arewa cikin kasashen dake taimakawa ta'addanci


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Shugaban Amurka ya sake mayar da Koriya ta Arewa cikin kasashen dake taimakawa ta'addanci, matsayin da ta samu lokacin shugabancin shugaba W.H. Bushi karin gwamnatin da ta shude ta cire sunanta

Amurka ta sake mayar da Koriya ta Arewa cikin jerin kasashen dake taimakawa ‘yan ta’adda a duniya bayan da aka jingine har tsawon shekaru goma, yunkurin da ka iya saka kasar cikin ‘karin matsin lamba ta kudi da diplomasiya.

“kamata yayi ace hakan ya faru tun shekarun baya,” a cewar shugaban Amurka Donald Trump, jiya Litinin daga fadar White House, yana mai kiran Koriya ta Arewa a matsayin mai tsarin mulkin kisan kai.

A yau Talata ne Baitulmalin Amurka a hukumance zai sanar da wannan kuduri da kuma jerin takunkumin da zasu biyo baya ga Koriyar, a cewar Trump. Sauran kasashen da ke a jerin kasaashen dake taimakawa ta’addanci sune Iran da Sudan da kuma Syria.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG