Amurka ta ce za ta gaggauta samar wa Najeriya jiragen yaki ‘yan yayi, kuma na zamani, wato A-29 Super Tucano, cikin lokaci. Daraktan sashin tsaro da hadin kai na sojin saman Amurka, Birgediya Janar Sean Ferrel, ya nanata hakan yayin da ya jagoranci tawagar da ta je Najeriya, inda su ka tattauna da manyan hafsoshin sojan saman Najeriya.
Janar Ferrel, ya ce za su yi duk wani abu mai yiwuwa wajen gaggauta samar da jiragen don ci gaba da fatattakar ‘yan ta'adda. Tunda farko sai da babban hafsan rundunar sojin saman Najeriya ya yaba da irin goyon bayan da Amurka ke ba su wanda ya ce hakan ya taka rawa wajen irin nasarar da aka cimma a yaki da ta'addanci.
Kakakin rundunar sojin saman Air Commodore Ibikunle Daramola ya nuna kwarin gwiwar samun wadannan manyan jiragen yaki zai taimaka a gama da burbushin ‘yan ta'adda a kasar.
Tuni dai masana akan harkokin tsaro irin su Air Commodore Baba Gamawa mai ritaya, ya ce ya na da kwarin gwiwar Amurka za ta cika alkawarin samar da jiragen akan lokaci.
Ga cikakken rahotan daga Hassan Maina Kaina:
Facebook Forum