Mai ba da shawara kan harkokin tsaron kasa a Amurka, John Bolton, ya gargadi babban alkalin kasar Venezuela, inda ya ce akwai “mummunan sakamakon” da zai iya biyo baya, bayan da babban jojin ya ba kotun kolin kasar umurni ta hana shugaban ‘yan adawan kasar Juan Guaido ficewa daga kasar.
Bolton ya ce, Amurka na Allah-wadai da barazanar da babban atonin kasar ke yi ga shugaba Juan Guaido, kamar yadda ya rubuta a shaifinsa na Twitter a jiya Talata, yana mai cewa, sakamakon da zai biyo baya, ba zai zamanto mai dadi ba, ga wadanda ke yi wa mulkin Dimokradiyya zagon kasa ko suka ci zarafin Guaido.
Atoni-janar na Venezuela Tarek William Saab, ya sake ba da umurnin a rufe asusun kudaden Guaido, yana mai cewa ana tuhumar shugaban ‘yan adawan ne kan irin ayyukan da yake yi akan gwamnatin shugaba Nicolas Maduro, wadanda suka saba doka.
Wadannan al’amura na faruwa ne bayan da hukumomin Washington, suka ayyana takunkumi akan kamfanin man fetur din kasar ta Venezuela na PDVSA.
Facebook Forum