Shugaban Amurka Donald Trump ya ce a kintse yake ya dauki zabin amfani da soji, wajen ladabtar da Korea ta Arewa, yayin da gwamnatinsa ta bayyana sabbin takunkumi a matsayin martani ga ayyukan gwaje-gwajen makamai masu linzami da kasar ke yi.
“A cikin shiri mu ke mu yi amfani da zabi na biyu, duk da cewa hakan bashi ne burinmu ba, bari na fada muku, idan har muka yi amfani da wannan zabi, wato abinda nake nufi daukan matakin soji, Korea ta Arewa za ta dandana kudarta.” In ji shugaba Trump.
Yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da Fira Ministan Spain, Mariano Rajoy a Fadar White a jiya Talata, Trump ya ce, ba za su bari Korea ta Arewa tana yi wa duniya barazana kan yadda za a rasa dumbin rayuka da ba za su misaltu ba.
Sabbin takunkumin na zuwa ne, a daidai lokacin da wani babban Janar din sojin Amurka, ya ce Korea ta arewa babbar barazana ce ga Amurkan, lura da yadda ya zama wajibi a fito a tunkari aikace-aikacen da ta ke yi na gina makamin nukiliya.
Facebook Forum