Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Amince Da Cinikin Jirgi Mai Saukar Ungulu Samfirin Apache Da KTK Akan Dala Biliyan $3.5


Apache Helicopter
Apache Helicopter

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta amince Amurka ta saida wa KTK jirage masu saukar ungulu da farashin shu ya kai dala biliyan $3.5.

Jiya Litinin, Pentagon ta ce ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta amince Amurka ta sayarwa koriya ta Kudu jirage masu saukar ungulu samfirin Apache da kayakin da yake bukata da rokoki da farashin su ya kai dala biliyan $3.5.

Cikin wata sanarwa, Hukumar hadin kan tsaron ta ce, ana kyautat zaton cewa, sayarda makaman zai taimakawa jamhuriyar Koriya ta Arewa kare kanta yanzu ta yadda zai karfafa ta kare kanta daga barazanar makiya nan gaba, sannan zai bata damar taka rawa a ayyukan yankin.

Bisa bayanan Pentagon, kamfanonin Boeing da Lockheed ne manyan ‘yan kwangilar da zasu kula da wannan cinikin.

Yayin da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta amince da cinikin makaman da Koriya ta Kudu, a wani bangare kuma, akwai wajibi ne sai an samu sahalewar majalisar dokokin kasar. Sanarwar cinikin makaman na zuwa ne a rana da Amurka da kasar ta Koriya ta Kudu suka kaddamar da atisayen sojin hadin gwiwa na shekara shekara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG