WASHINGTON D.C. —
Amurka na shirin tura karin dakaru da makaman kare hare-haren sama zuwa Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, a cewar ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon.
Wannan sanarwa na zuwa ne, bayan hare-haren da aka kai kan matatun man kasar ta Saudiyya, wadanda Amurka ta ce Iran ce ta kai su, zargin da hukumomin Tehran suka musanta.
Sakataren tsaron Amurka, Mark Esper ne ya bayyana shirin tura karin dakarun, yayin wani taron manema labarai da aka yi a Pentagon a jiya Juma’a, matakin da ya ce tuni Shugaba Donald Trump ya amince da shi.
A cewar Hafsan hafoshin dakarun Amurka, Janar Joseph Dunford, a karshen makon nan za a tattauna tsarin da za a bi wajen tura dakarun zuwa Saudiyya, wanda za a fitar a mako mai zuwa.