Tsohon jakadan kasar Birtaniya a Amurka, ya yi ammar cewa, janyewar da shugaban Amurka Donald Trump ya yi daga matsayar da aka cimma kan nukiliyar Iran, “babbar barnace ta fuskar diplomasiyya” da shugaban ya yi ga abin da tsohon shugaban Amurka Barack Amurka ya bari a baya, a cewar wasu sabbin bayanai da aka kwarmata, wadanda wata jaridar kasar ta Birtaniya ta wallafa.
Jaridar The Mail ce ta wallafa sabbin bayanan a yau Lahadi, wadanda tsohon jakada Kim Darroch ya aika.
A makon da ya gabata, jaridar ta wallafa wasu bayanan da aka kwarmata, wadanda suka nuna Darroch yana muzanta Shugaba Trump da gwamnatinsa.
A ranar Larabar da ta gabata kuma, Darroch ya sauka daga mukaminsa bayan bullar bayanan na sirri a baina jama’a, lamarin da ya sa Shugaba Trump ya shiga shafinsa na Twitter ya kira Darroch a matsayin “shasha mai ji-ji da kai”, ya kuma ce gwamnatinsa ba za ta kara hulda da shi ba.
Su dai wadannan bayanai da aka wallafa a jaridar, sakonni ne na waya da manyan jami’an kasar Birtaniya ne kadai ya kamata su karanta.