Hukumomin Amurka sun baiwa wadanda suka fita zanga-zanga shawara da su je su yi gwajin cutar COVID-19, bayan da suka kwashe sama da mako guda suna yin tattaki tare da yin cudanya da juna.
Gwamnan jihar New York Andrew Cuomo, ya ce za su bude wasu sabbin cibiyoyin gwajin cutar guda 15, inda ya yi kira ga wadanda suka shiga zanga zanga da kada su dauki abin da wasa.
Hakazalika hukumomi a biranen Atlanta, San Fransisco da Seattle duk su ma sun yi makamancin wannan kira ga jama’ar da suka fita zanga zanga kan mutuwar George Floyd da su ma su yi gwajin.
A yau Litinin a ke sa ran sama da mutum dubu 400 za su koma bakin aiki a New York, birnin da ya fi kowanne yawan jama’a a Amurka.
Wannan shi ne zangon farko na maido da al’amuran yau da kullum a birnin.
Hakazalika, wannan zai zamanto karo na farko ga jama’ar da za su dunguma zuwa tashoshin jiragen kasa cikin wata uku da aka kwashe ba a fita.
Sai dai dubban gidajen cin abinci da ke birnin za su ci gaba da kasancewa a rufe akalla zuwa karshen watannan.
Facebook Forum