Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ambaliyar Ruwa Tayi Barna a Jihar Jigawa


 Sule Lamido gwamnan jihar Jigawa
Sule Lamido gwamnan jihar Jigawa

Wani mamakon ruwan sama da aka samu a jihar Jigawa yayi sanadiyar ambaliyar ruwan da ya rushe gidaje da dama a wasu garuruwa.

Ambaliyar ruwan ta bata dakuna a garuruwan Ringim da Taura da Hadeija da kuma Dutse babban birnin jihar.

Kidigdiga ta nuna dakuna dubu biyu da dari uku suka rushe a garin Ringim da wani kauye kusa da garin. A Taura kuma dakuna dari shida da goma ne suka rushe kana a Dutse an samu rushewar dakuna dari hudu da tasa'in da uku. A garin Hadeija kuma ambaliyar ta lalata dakuna dari uku da sha uku.

Alhaji Ahmed Mahmud Gumel mataimakin gwamnan jihar kuma shugaban kwamitin gwamnati domin tallafawa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa yace an samu barnar dakuna dubu uku da dari bakwai da goma sha takwas. Duk wadanda gidajensu suka zube suna cikin ginin makaranta inda ake ciyar dasu da kuma basu duk wani abu na taimaka ma rayuwasu. Yace wannan ba shi ba ne na farko ba. Dama daidai wannan lokacin akan samu ambaliyar ruwa. Gwamnati tana shigowa ba ta bayar da abinci da wasu taimako kafin a basu kudade su koma su sake gina gidajensu.

Dangane da lokacin da wadanda ambaliyar ruwan ta tagaryara zasu samu taimakon sake gina muhallansu sai mataimakin gwamnan yace ana hada rahoto wanda za'a yi anfani dashi. Da sun samu rahoton zasu yi aikin cikin tsanaki kuma tsakaninsu da Allah. Babu cutar wani ko cutarwa a ciki.

Alhaji Ahmed Gumel yace a duk shekara gwamnati na daukan matakan dakile barnar ambaliyar ruwa bayan ga wayar da kawunan jama'a akan ambaliyar. Tun lokacin da suka shigo mulki kowane gari sun fitar da titi da yin kwalta da magudanar ruwa. Sabili da haka an samu sauki da dama. An kuma karfafa tsafta tare da share wuraren da suke da kazanta da bude hanyar ruwa da ta toshe. Ya kira jama'a cewa su lura, wasu ayyuka ba sai gwamnati tayi ba. Su mayar da hankali. Su duba inda ruwansu ke bi su gyara da kansu.

Jihar Jigawa na cikin jihohin dake fama da ambaliyar ruwa kowace shekara kuma masana na ganin lokaci yayi da jihar zata lalubo bakin zaren warware matsalar. Amma mataimakin gwamnan yace akwai yanay biyu a duniya. Akwai sanyi kuma akwai zafi. Idan an samu zafi mai tsanani kankara dake can wata kasa zata narke ta zama ruwa da zai fito ya ci duniya. Wuraren da ruwa baya ci a da zai ci. Wadannan abubuwa daga Allah suke. Babu wani gari a duniya yanzu da ba zai iya samun ambaliyar ruwa ba.

Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG