Cutar ta fara addabar mutane ne tun 'yan wasu watanni da suka gabata.
Jami'an kiwon lafiya na jihar sun ce kawo yanzu mutane 538 ne suka kamu da cutar. Mutane 42 kuwa cikinsu sun rigamu gidan gaskiya.
Dr Usman Muhammed darakta a matakin farko na ma'aikatar kiwon lafiya ta jihar yace suna da masaniya akan barkewar cutar. Yace sun yi iyakacin kokarinsu. Sun basu magunguna an taimaka masu. Wadanda suka mutu wadanda suka bata lokaci ne kafin su isa inda zasu samu taimako.
Har yanzu dai cutar na cigaba da bulla a wasu sassan jihar. Wani daga karamar hukumar Mariga, Yahaya yace sun samu barkewar cutar amai da zawo. Yace cutar na ta kama mutane fiye da yadda ake zato.
Dr Usman ya bayyana matakan da suka dauka. An yi gangami an rubutawa kowace karamar hukuma an sanar dasu da abubuwan dake faruwa game da zawo da amai. An gargedsu su taimaka da magunguna da ma'aikata.
Matsalar rashin ruwan sha mai kyau da tsaftace muhalli na cikin abubuwan dake haifar da cutar.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.