Gidaje kimanin dubu 40 sun lalace, bayan da aka sheka ruwa mafi tsanani a tarihin Baron Rouge. Jami'an Hukumar Aikin Agajin Gaggawa ta (FEMA) da masu kai gudunmowa sun kasance a wurin na tsawon kwanaki, kamar yadda 'yan agajin Red Cross su ka yi.
"Daidai ne a ce wannan jaha ta saba da guguwa mai ambaliyar ruwa," a cewar Craig Cooper na hukumar Red Cross ga Muryar Amurka, wanda ya kara da cewa, "to amma wannan wani irin ruwan sama ne innanaha, kuma abin da mu ka ji shi ne a sassa da dama, al'ummomi ba su taba ganin ambaliyar ruwa ba, ko kuma rabon su ga ambaliya irin wannan tun shekaru 30 da su ka gabata."
Cooper ya yi gargadin cewa har yanzu al'amarin na Baton Rouge Rouge na cigaba da daukar sabon salo, a yayin aka cigaba da ayyana wurare yankunan da ke karkashin dokar ta baci, ana ganin karin baran da kuma karuwar mace-mace.
An ceto mutane 30,000 tun daga ranar Jumma'a.