A Turkiyya hukumomin kasar suna shirin zasu saki fursinoni dubu 38,wanda suke da kasa da shekaru biyu kamin su kammala wa'adin zaman gidan kason. Sanarwar da aka bayar yau Laraba, tana zaman wani bangare ne na dokar da aka kafa yau da zummar samar da fili ga mutane da aka kama baya-bayan nan kan zargin suna da hannua juyin mulkin da aka yi wanda bai sami nasara ba.
MInistan shari'a na kasar Bekir Bozdag ne ya bayyana haka a sakonni da ya aike ta shafin Twitter. Yayi kashedin cewa sakin ba afuwa bace, illa dai an saki fursinonin da sharadi.
Baya ga wadannan fursinonin wadanda suke da kasa da shekaru biyu kamin su kammala zaman fursina, fursinoni da suka yi fiyeda rabin daurin da aka yanke musu, suma zasu amfana a karkashin wannan shiri.
Sai dai dokar ba zata shafi fursinoni wadanda suka yi kisa,ko ta'adanci, cin zarafin iyalansu, ko wadanda aka daure domin sun yi fyade.
An kashe akalla mutane 270 ranar 15 ga watan Yulin da ya wuce, sakamakon juyin mulkin da bai sami nasara ba a kasar.