Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Alkaluman Hukumar Kididdigar Najeriya Na Cewa Mizanin Hauhawar Farashi Ya Kai Kaso 28.9 Cikin 100


Kayan masarufi a wata kasuwar Abuja a Najeriya
Kayan masarufi a wata kasuwar Abuja a Najeriya

Hakan na kunshe ne a cikin rahoton hukumar kididdigar na watan disambar shekarar 2023 dake bin diddigin hauhawar farashin kayayyakin masarufi da aka fitar a jiya litinin.

Wata alkaluma da Hukumar Kididdigar Najeriya wato NBS ta fitar ya ce mizanin hauhawar a kasar a halin yanzu ya kai kaso 28.9 cikin 100

Rahoton yayi la’akari da yanayin sauyawar farashin kayayyakin abinci da na ayyuka. Gabanin fitar da rahoton na ranar litinin, hauhawar farashin Najeriyar na kan kaso 28.20 cikin 100 a watan Nuwambar 2023.

Hukumar kididdigar ta NBS ta wallafa cewar “duba da irin wannan sauyi, mizanin auna hauhawar farashin ya nuna samun karuwar kaso 0.72 cikin 100 a watan disambar 2023 idan aka kwatanta da yadda yake a watan Nuwambar daya gabace shi”.

NBS ta ci gaba da cewar, “har ila yau, a bisa kididdiga ta wata-wata, mizanin hauhawar farashin a watan disambar 2023 ya kai kaso 2.29 cikin 100 inda ya dara na watan nuwambar daya gabace shi wanda ya kai kaso 2.09 cikin 100 da kaso 0.20 cikin 100. hakan na nufin cewar, mizanin auna matsakaicin hauhawar farashi a watan disambar 2023 ya dara na watan nuwambar daya gabace shi”.

Hauhawar farashin kayan abinci ya sake hawa a watan da ake magana akai.

Hukumar ta NBS ta iyakance hauhawar farashin a bisa kididdigar shekara-shekara akan kaso 33.93 cikin 100, wanda ya dara kididdigar da aka gudanar a watan disambar 2022 (wanda ya kai kaso 23.75 cikin 100) da kaso 10.18 cikin 100.

A na ci gaba da samun hauhawar kayan abinci a Najeriya watanni 6 bayan da Shugaba Bola Ahmad Tinubu ya ayyana dokar ta baci akan samun wadatar abincin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG