An lura cewa rashin yalwataccen masauki mai inganci Ga alhazan Najeriya na daga wasu matsalolin da alhazan ke fuskanta dangane da zamansu a wasu wurare masu muhimmanci, da bai ba su damar gudanar da ayyukan ibada cikin walwala, da tsabtar yanayi, da kuma kwanciyar hankali.
A taron da ya gudana da manyan kafofin yada labarai na duniya a birnin Makka, bayan ziyarar ganewa ido, gwamnan Bauchi Bala Abdulkadir Muhammed, Kauran Bauchi, ya bukaci gwamnatin Najeriya da ta Saudiya, da su sake sabon lale akan batun masaukin alhazan Najeriya.
A hirarsu da manema labarai na kasashen waje, bayan ziyarar tantance masaukan 'yan Najeriya, gwamna Bala Abdulkadir Muhammed Kauran Bauchi, ya ce yadda ya ga 'yan Nariya suke zaune, abin ya bata masa rai tare da ba shi tausayi.
Ga cikakken rahoton daga wakilin Muryar Amurka Abdulwahab Muhammad.
Facebook Forum