Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Albashin 'yan Siyasar Najeriya Yafi Na Sauran Kasashe - Inji Ma'aikata


Ma'aikata a Najeriya
Ma'aikata a Najeriya

Ma'aikata a fadin Najeriya sun yi bukin ranar ma'aikata ta duniya, wasu da dama sun koka da cewar albashin da ake biyan 'yan siyasar kasar ya fi na sauran kasashen da suka daurewa demokaradiyya gindi.

Yau ce ranar ma’aikata a Najeria, kuma an ware kusan Naira BIliyan uku da rabi domin sallamar shugaban kasa mai barin gado GoodLuck Ebele Jonathan da mataimakin sa da kuma sauran ‘yan majalisu da kuma masu rike da mukaman siyasa a matsayin kudaden sallama daga aiki bayan kasa samun nasarar zaben da ya gabata.

Bada sanarwar fitar da wadannan makudan kudade yazo daidai ne da lokacin da ma’aikatan Najeriya suka bi sahun sauran ma’aikata a kasashen duniya daban daban wajan gudanar da ranar ma’aikata.

Wasu daga cikin ma’aikatan sun koka da cewa kudaden da ake biyan ‘yan siyasar ta Najeriya ya fi na wasu sauran kasashen duniya da suka daurewa demokaradiyya gindi.

Fatan ma’aikan dai shine kawo karshen kashin dankalin da ake yi ma kananan ma’aikata da kuma sauran talakawa da ma cika alkawuran da gwamnati mai shudewa tayi masu. Da kuma fatan samun canji wurin sabuwar gwamnati mai jiran gado.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG