A wassanin kwallon kafa na jaha - jaha na kasar Faransa kuwa, wani wasa ne da ya wakana a karshen makon jiya ya kawo rudani, inda Arles Face yayi wa Septemes ci 22-1. Wannan nasara ce ta bai wa clun Arles Face damar jan ragamar rukuninsa, saboda tseraya yawan cin kwallayen raga gaban yan kwallon Martigues.
Wannan ya haifar da shakku da ma zargin yin sarande a wannan karawar, inda tuni hukumar kwallon kafa mai kula da kankanan azuzuwa ta kasar Faransa ta kafa kwamitin bincike game da wannan karawar.
A dai wassanin kwallon kafa, ba kasafai ba, a ke ganin irin wannan ruwan kwallaye ya samu a karawa guda ta wasan kwallon kafa.
Ita ko hukumar kwallon kafa ta nahiyar Afurka CAF ko CAF, a yau talata ne ta bada sanarwar zabar kasar Morocco domin karbar bakuncin karo na karshe, na wasan kofin Champions league na Kwallon kafa na nahiyar Africa na bana.
Hukumar dai, bata bayyana ko a wane gari ne ba a kasar Morocco za a gudanar da wannan karawar ta karshe, amma ta sake zaben wata kasa ne, bayan da kasar Senegal ta yi jifa da wannan tayin, yayin da kasar ta Morocco ce kawai ta saura daga cikin wadanda suka bukaci karbar bakuncin wasan.
Za a yi karawar karshe ta bana ta wasan kwallon kafa ta Champions league ta bana ne ta nahiyar Afurka a ranar 30 ga watan Mayun da muke ciki idan Allahu ya kai mu.
Yanzu haka dai a wannan kombalar, a karon kusa da na karshe karo na farko, kungiyar kwallon kafa ta kasar Morocco, Widad Kasablanca, ta yi wa Petro Luanda 3 - 1 a Luanda, yayin da Al Ahly ta kasar Misira ta wa Entente Setif ta kasar Algeria ci 4 - 0 a karawar su ta farko.
Saurari rahoton Harouna Mammane Bako: