Jamila Ado Mai Wuka – wacce ta hallarci shafin DandalinVOA a bara ta kuma nuna cewar tana sa ran fitowa a fim din Bilkisu, wato wani fim mai nisan zango a yanzu, ta canza ra’ayinta sakamakon sauya akallar fina-finai a yanzu.
Mafi yawan fina-finan sun fi mai da hankali ga fim na soyayya sabanin kawo wata matsala da ta ke adaban mutanen domin kawo musu gyara, ta kara da cewar inda son samun tane a wancan lokacin shine ta so ta sami gurbi a masana’antar Kannywood.
Malama Mai Wuka ta ce a yanzu sun fi yin fim na soyayya kuma idon mutane bai bude sosai ba, ta fi so a yi fina-finai na al’ada da kuma abubuwan da ke damun alumma, ta sauya salon wakarta ma a yanzu sabanin yadda ta ke yi a da.
Jamila ta ce har yanzu ta na waka kamar yadda aka santa a da sai dai a yanzu ta fi yin wakokin siyasa ne, ko na biki domin a cewarta sun fi saurin kawo kudi, ta yi waka da sauki a da, amma a yanzu kuwa iya kudinka iya shagalinka.
Baya ga waka kuma takan taba hajja domin a ta bakin mawakiyar ba’a tsayawa a waje guda, sai ana wasu harkokin da zasu rike mutum.
Facebook Forum