Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Banbanci Tsakanin Kalamun Neman Zabe da Na Shugabanci- Obama


Shugaban Amurka Barack Obama mai barin gado
Shugaban Amurka Barack Obama mai barin gado

Yayinda yake neman zabe sabon shugaban Amurka Donald Trump yayi wasu kalamu ba kakkautawa wadanda suka tsoratar da mutane kana suka harzuka wasu, lamarin da ya kara kawo rabuwar kawunan jama'ar kasar

Shugaban Amurka mai barin ado Barack Obama yace nan bada jimawa ba sabon shugaban da zai gaje shi, Donald Trump zai gane cewa akwai banbancin tsakanin suruttai ba kakkautawa a lokacin yakin neman zabe, da wainar da ake toyawa da zaran mutum ya hau kan karagar mulkin shugabancin Amurka.

A haduwarsa da manema labarai jiya, wacce kuma itace ta farko tun gagarumar nasara mai ban mamaki da Trump ya samu a zaben da aka yi a makon jiya, shugaba Obama yace yana jin Trump zai zame hazikin shugaba muddin yana tareda mutanen kirki a zagaye da shi.

Shugaba Obama yace zai bar Amurka cikin kyakyawan hali nagari fiyeda yadda ya same ta, kuma yana da karfin imanin cewa Trump zai aiwatarda manufofi masu anfani.

A jiyan ne kuma shugaba Obama ya bar Amurka a tafiyarsa ta karshe a wa’adin mulkinsa, inda zai ziyarci kasashen Girka, Jamus da kuma Peru.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG