Girgizar kasar mai karfin maki 2.9 ta auku ne kilomita 23 daga Sungibaem, yankin da Korea ta Arewan ta yi gwaje-gwajen makamanta na nukiliya, in ji hukumar ta Amurka.
“Lamarin na da alama da girgizan kasa, amma kuma ba za mu iya yanke hukuncin cewa ya faru ne da gaske ko kuma sanadiyar wasu aikace-aikacen dan adam ne ba,” hukumar ta kara da cewa.
Gwajin makamin nukiliyan da Korea ta arewan ta yi na karshe a ranar 3 ga watan Satumba, ya haifar da girgizan kasa mai karfin makin 6.3.
Sai dai ba lallai ba ne a ce a duk lokacin da kasa ta kada, ya zama cewa an yi gwajin makamakin nukiliya, domin a ranar 23 watan Satumba, an dauka wata ‘yar girgizar kasa da ta auku a yankin, na da nasaba da burbushin gwajin makamin nukiliyan da Korea ta arewa ta yi a farkon watan, amma ashe ba haka bane.
Facebook Forum