Aisha Sani Bala, wacce aka fi sani da Adama a shirin drama na Rediyo wato 'Birnin Dala' inda ta ke fitowa a matsayin Fulani matar Waziri a cikin wasan kwaikwayo na Birnin Dala wanda suke nishadantar da masu sauraro.
Ta ce ta tsinci kanta a wannan wasan kwaikwayon biyo bayan aiki a wani gidan rediyo, inda a wani yunkurinsu na tabbatar da sun tafi da masu sauraronsu ne suka fito da wannan sabon wasan kwaikwayo mai suna Birnin Dala a Kanon Dabo.
Fulani Adama ta ce bata sha’awar a nan gaba ta fito a wasan kwaikwayo na fili, son samun ta dai ta fito ne a wasan kwaikwayo na boye ko na bayan fagge, wato ta akwatin rediyo inda mai sauraro ba zai santa ba, sai da ya san muryar ta ta akwatin rediyonsa.
Daga cikin kalubalen da ta ke fuskanta kasancewar ita ma’aikaciyar gidan rediyo ce, kuma wasan kwaikwayo inda ta ke aiki ne suka kirkiri shirin, suka kuma fito da shi, a wasu lokutan sai tana tsaka da aiki kwatsam sai a ce ta zo su dauki wasan shirin Birnin Dala.
Ta kara da cewa tsarawa da shirya fim din duk a gidan rediyon nasu aka hada shi, sannan sun dauki wasan tamkar wani shiri ne na mussaman da suka kirkira, sannan a wasu lokutan akan tallata wasu daga cikin wadanda zasu fito a wasan kwaikwayon domin su zo a tantannce domin su sami damar shiga wannan wasa.
Daga karshe ta ce babban burin ta shine ta zama wata jajirtacciyar 'yan jarida, kamar ire iren 'yan jaridar da suka ta ka rawa a cikin alummarsu alal misali kamar Femi Oke ta tashar Alzajeera.
Facebook Forum