Na rasa masoya ta sandiyar sana’ar da na zaba wa kai na waka, inda na so na aure wata yarinya da muka yi soyayya da ita, aka kuma hana ni aurenta sanadiyyar wani kallo da ake yi min na rashin da’a, da daraja ta mawaki, mawaki Ahmad I Ahmad.
A wannan lokaci mutane sukan yi rade-radin cewar yaya za’a baiwa mawaki aure? alhalin ana yi musu kallon marasa tarbiya, a cewarsa hana shi da aka yi sai da ya taba masa zuciya, tare da jan hankalin al'umma da su dinga bincike kafin zartar da hukunci.
Ahmad I. Ahmad, mawaki kuma mai shiryawa a fanni na wakokin mussaman ma ga mawaka da zarar sun bukaci hakan, ma’ana ya tace tare da inganta wakar mawaki, wanda ya shafe kimanin shekaru goma yana wannan masana’antar.
Ahmad ya kara da cewa sanadiyar waka ya ce ya gina studio dinsa, inda yake wakoki da talla ga mutane, ya kara da cewa daga cikin kalubalen da ya fuskanta na mutane ne da suke cewa, Ahmad mai shiru ne ya dauka waka ta rago ne, sai ga shi yadda suke raina wa kwazonsa ya samu nasarori da dama ta waka.
Facebook Forum