Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ahmad Ahmad Ya lashe Zaben Hukumar Kwallon Kafa Ta Afirka


A yau Alhamis 16 ga watan Maris, 2017 aka zabi Ahmad Ahmad, a matsayin sabon shugaban hukumar kula da kwallo kafa ta Afirka.

An gudanar da zabenne a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha
inda Ahmad, na kasar Madagascar, ya doke Dadadden shugaban hukumar ta CAF Isa Hayatou, dan kasar Kamaru.

Ahmad, ya lashe zabenne da rinjayen kuri'u 34 daga cikin 54, da aka kada.

Wannan zabe shine sauyi na farko da akayi tun bayan darewar Isaa Hayatou, na kasar Kamaru da ya karbi mulkin a shekarar 1988.

Ahmad, dai zai kasance shugaban hukumar na bakwai a shekaru 60 a tarihin CAF.

Nasarar da ahmad, ya samu wani gagarumin sauyi ne ga kwallon kafar Afirka
Haka kuma hayatou, dan shekara 70, da haihuwa zai rasa matsayinsa a hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa da na gudanarwarta.

Sau biyu yana karawa da wasu 'yan takarar a zaben shugabancin hukumar kuma a duk lokuta biyu yana samun gagarumar nasara.

Sai dai wannan karon kuri'u 20, kacal ya samu, acikin 54, da aka jefa wanda ya kawo karshen fatan da yake yi na yin nasara a karo na 18 a kan matsayin, wanda zai bashi damar shugabancin hukumar a cikin shekara 29..

Ahmad Ahmad, kafin samun nasararsa a wannan zaben shine shugaban kungiyar kwallon kafa ta Kasar Madagascar.

Ga jerin sunayen mutane bakwai da suka reke wannan kujera
Abdel Aziz Abdallah dankasar (Egypt) 1957-1958
Abdel Aziz Mustafa (Egypt) 1958-1968
Abdel Halim Mohamed (Sudan) 1968-1972
Ydnekatchew Tessema (Ethiopia) 1972-1987
Abdel Halim Mohamed (Sudan) 1987-1988
Issa Hayatou (Cameroon) 1988-

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

  • 16x9 Image

    Bala Branco

    Bala Branco ma'aikacin jarida ne a Albarka Radio FM Bauchi dake tarayyan Najeriya wanda yake shirya wa Dandalin VOA labaran wasanni, Haifaffen Unguwar Nufawa ne dake birnin Bauchi. Mazaunin Bauchi a Najeriya.

XS
SM
MD
LG