Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Arsene Wenger ya bukaci shuwagabannin gudanarwa na kungiyar da su bashi mako uku domin yayi tunanin yuwar sabunta kwangilarsa a kungiyar ko kuma yayi gaba Wenger dai ya shafe shekaru sama da goma sha takwas a Arsenal a matsayin mai horas da ‘yan wasa ba tare da ya lashe wasu muhimman kofuna ba.
A satin da ya gabata ne Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta kasar jamus, tabi Arsenal har gida ta lallasata da kwallaye 5-1 a gasar cin kofin zakarun nahiyar turai UEFA Champion League na shekara 2016/2017 a matakin zagaye na sha shida a karawarsu na biyu, Inda a karawarsu ta farko a can kasar Jamus , anan ma Arsenal ta sha kashi da 5-1 wannan yasa aka cere kungiyar ta Arsenal a gasar.
Arsene Wenger zai kamala kwangilarsa a kungiyar ta Arsenal a shekara ta dubu biyu da sha takwas.
Har ila yau kungiyar kwallon kafa ta Chelsea zata fafata da takwararta Manchester United à yau bangaren cin kofin kalubale na kasar Ingila 2016/2017 a matakin wasan zagaye na kusa da na kusa da na karshe watau (Quarter Final) za'a buga wasanne da misalin karfe tara saura kwata na dare agogon Najeriya Nijar Kamaru da Kasar Chadi.