Idan har kasar Marocco ta janye kanta ga karbar bakuncin gudanar da wasan cin kofin Afirka wato (African Nations Cup) a watan Janairu saboda annobar cutar Ebola, to Afirka ta Kudu ba’a shirye take ba wajen karbar bakuncin wannan wasan inji ministan wasanni Fikile Mbalula.
Kungiyar tarayyar kwallon kafa ta Afirka nata tuntubar kasashe kamar Afirka ta Kudu, Ghana dakuma sauran kasashe biyar tun kafin watan Nuwamba, kuma an zauna wasu taron tautaunawa har guda biyu domin yanke hukunci kan kasar da zata karbi bakuncin wasan mai zuwa.
Ministan wasannin dai yace ya gayawa kafofin wasa labarai na Afirka ta Kudu cewa Kasar nada alhakin taimakawa wajen yakar cutar Ebola data kashe sama da mutane 4,500 a yammacin Afirka.
Yakuma kara dacewa tun kafin a dauki wannan magana ga hukumomi, zan iya gaya muku cewa karbar bakuncin wannan wasa ba’abune mai yiwuwa ba.
Kasar Afirka ta Kudun dai na daya daga cikin kasashe bakwai da kungiyar wassan ta Afirka ta ke ganin za’a su iya karbar bakuncin wasannin idan har Morocco ta janye kanta.
Duk da yake kasar ta karbi bakuncin wasanni biyu abaya na bazata, ta karba a shekara ta 1996 lokacin da kasar Kenya ke fuskantar rashin kudi, saikuma na shekarar data wuce inda kasar Libya ke fama da rikice rikice a kasar.
Jami’an gwamnatin Moroccon dai a karshen satin nan sunce suna son a dakatar da wasannin daga sha bakwai ga watan Janairu zuwa takwas ga watan Febarairu saboda suna tsoron yaduwar kwayar cutar Ebola.