Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An yi Waje da Koch din Super Eagles Stephen Keshi


Stephen Keshi
Stephen Keshi

Algeria da Cape Verde sun kasance kasashen farko da suka fara hayewa, a gasar fidda gwani, na cin kofin nahiyar Afirka.

Najeriya,da yanzu ke rike da kofin bata tabuka abun a zo agani ba, a gasar fidda gwanin.

Hukumar kwallon kafa ta Najeriya, a yau alhamis, ta sanar cewa ta sallami, Koch din kungiyar, Super Eagles, Stephen Keshi, da mataimakinsa Emmanuel Amokachi, da kuma Ike Shorounmu, mai kula da mai tsaron gida.

Wannan ya biyo bayan nasarar farko da Super Eagles, ta samu a jiya inda ta doke Sudan da ci 3 da 1 .

An dade ana cacar baki a Najeriya dangane da sabonta kwantragin Stephen Keshi, tun bayan gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar Brazil.

Amma a yanzu tsohon mai kula da kungiyar ta Super Eagles, Amodu Shaibu,shi zai kula da kungiyar, kafin a samo wani daga kasar waje.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG