'Yan kallo su kimanin dubu casa’in suka makare filin wasa na Soccer City dake dab da unguwar bakar fata ta Soweto a Johannesburg a yau jumma’a domin kallon wasan farko na gasar cin kofin duniya ta 2010, inda Afirka ta Kudu mai masaukin baki ta yi kunnen doki da kasar Mexico.
Wannan shi ne karon farko da ake gudanar da gasar cin kofin kwallon kafar manya ta duniya a nahiyar Afirka.
Manyan baki da dama sun halarci wasan na farko da aka buga a bayan bukukuwan budewa, cikinsu har da shugaba Jacob Zuma na Afirka ta Kudu da shugaba Felipe Calderon na Mexico da mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden.
Hotunan telebijin sun nuna Archbishop Desmond Tutu mai ritaya, wanda ya taba lashe lambar yabo ta Nobel, yana taka rawa sanye da kaya irin na ‘yan wasan Afirka ta Kudu.
Abinda kawai ya rage ma bukukuwan bude wannan wasa armashi shi ne rashin halartar tsohon shugaba Nelson Mandela, wanda ya soke zuwa bukin a saboda wata tattaba-kunnensa wadda ta rasu a hatsarin mota cikin daren jiya a lokacin da take komawa gida daga wani bukin marhabin da masu halartar gasar.
A karawa ta biyu a yau din dai, yanzu haka Faransa tana gwabzawa da ‘yan wasan kasar Uruguay a birnin Capetown.