Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Addu'ar Uku Ta Marigayi Yahaya Mahmud


Yahaya Mahmud
Yahaya Mahmud

A garin Kaduna an yi addu'ar uku ta marigayi Yahaya Mahmud fitaccen lauya a jihar Kaduna wannda Allah ya yiwa rasuwa.

'Yan uwa da abokan arziki na Lauya Yahaya Mahmud na cigaba da karbar gaisuwar rasuwarsa yayin da aka yi addu'o'in uku a gidan marigayin a dake garin Kaduna.

An haifi Lauya Yahaya Mahmud a garin Kachia cikin jihar Kaduna ranar takwas ga watan Maris na shekarar 1952. Ya yi karatun sakandarensa a makarantar Al-Huda Huda dake Zaria. Kana ya yi karatun digiri na lauya a Jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. A shekarar 1978 ya je makarantar koyan aikin Lauya dake Legas. A shekarar 1981 ya je Jami'ar Oxford dake Ingila.

Ya fara aiki a matsayin babban akawu a ofishin gwamna a Kaduna a shekarar 1970. Bayan shekaru uku ya zama ragistara a babban kotun Kaduna, kana ya zama babban alkali a shekarar 1979. A shekarar 1990 ya bude cibiyar aikin lauya ta kanshi.

Abdulrauf Atiku lauya ne da ya yi aiki na tsawon zamani da marigayin kuma shi ne ya yi maganar karshe da shi. Ya ce da ya dawo daga Abuja ya shiga ofishinsa ya sanarda shi cewa ya dawo. A kan haka ya bashi wasu wasiku da wata jarida ya je ya shirya wata wasika dangane da aikin da Alhaji Modu Shafiff ya bashi. Abdulrauf ya ce da ya karbi wasikun ya ce ya fara aiki sai ya tuna bai tambayi marigayin ba mutane nawa zai rubutawa. Ko da ya shiga ofishin sai ya sameshi yana barci a kan kujera. Bayan mintuna talatin da ya koma ya sake samunsa hakan. A lokacin ne ya san rai ya yi halinsa.

Isah Lawal Ikara nada cikakken bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:48 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG