Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Yahya Nguroje, ya ce tuni aka baza komar farautar 'yan bindigan da suka sace wadannan mutane.
Wannan matsala ta sace mutane domin neman kudin fansa, yanzu haka na neman gagarar kundila a Najeriya, al'amarin da yasa hukumomin tsaro hada kai, da shugabannin kungiyoyin sakai ciki har da na Fulani makiyaya irinsu Miyetti Allah da Tabital Puulaku.
To sai dai kuma, ya yin da wasu ke taimakawa yanzu haka 'yan bindigar sun fara bin wasu shugabanin kungiyoyin Fulanin har gida suna kashewa, kamar wanda ya faru cikin kwanakin nan, inda aka kashe wani fitaccen shugaban kungiyar Tabital Puulaku, na jihar Adamawa, Abdu Bali.
Muhammad Jika Buba, kakakin kungiyar Miyetti Allah a jihar Adamawa, ya ce duk da kisan da ake yiwa shugabanin, babu wani kulawa da iyalan wadanda aka kashen ke samu daga hukumomi, batun da ya ce yanzu jikinsu ya yi sanyi.
Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdul'aziz.
Facebook Forum