Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu Cutar Covid-19 Sai Karuwa Yake a Amurka


Wasu likitoci da wani mai jinya a asibiti
Wasu likitoci da wani mai jinya a asibiti

A karon farko a Amurka tun farkon bullar annobar coronavirus, kasar ta cimma sabbin kamuwa da COVID-19 dubu 50 a wuni guda.

A sabbin alkaluman da aka bayyana a jiya Laraba,. Jihar Carlifonia ce ke kan gaba bayan da bayyana sabbin kamuwa da cutar dubu 9,740, bisa ga bayanin wani shirin bin didigin COVID-19 da mujallar Atlantic Magazine ke tafi da shi, sannan sai jahar Texas ta kudu maso yamma mai sabbin kamuwa dubu 8,076.

Jahar Florida ta kudu maso gabashi ta kasance ta uku da sabbin kamuwa dubu 6,563, yayin da Jahar Arizona ta kudu maso yammaci kuma ta rufe da sabbin kamuwa dubu 4, 877.

Yadda ake yi wa wani gwajin Cutar Coronavirus a asibiti.
Yadda ake yi wa wani gwajin Cutar Coronavirus a asibiti.

Sauran jihohin aka samu sabbin kamuwa da COVID-19 masu yawa a wuni daya a jiya Laraba, sun hada da Alaska, Georgia, Louisiana, North Carolina da Tenessee.

Bayan wadannan sabbin alkaluma masu yawan kuma, an samu sabbin alkaluman wadanda aka kwantar a jihohi 8 inda Texas ta bada rahoton kwantar da mutane dubu 6,904 a jiya Laraba. Lamarin da ya haifar da tashin hankali a daya daga cikin jahohi mafiya girma a kasar, inda wasu asibitocin suka kusan cika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG