Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adadin Masu COVID Ya Haura dubu 150 a Najeriya Yayin Da Aka Fara Allurar Riga-kafi


Lokacin da aka fara yi wa ma'aikatan lafiya allurar riga-kafin coronavirus a Najeriya
Lokacin da aka fara yi wa ma'aikatan lafiya allurar riga-kafin coronavirus a Najeriya

Bayanan da hukumar dakile yaduwar cututtuka ta NCDC ke fitarwa a Najeriya sun nuna cewa adadin masu harbuwa da cutar coronavirus ya haura mutum dubu 150.

Hukumar ta NCDC ta wallafa wadannan alkaluma ne a shafinta na Twitter inda ta bayyana cewa yanzu Najeriya na da mutum 158, 237 da cutar ta harba ya zuwa ranar 6 ga watan Maris.

Wannan sabon adadi ya kai wannan mizani ne, bayan da aka samu karin mutum 195 da cutar ta harba a wannan rana a sassan kasar.

A jihar Legas an samu mutum 70, 22 a Kaduna, 18 a Abia, 10 a Kano yayin da Akwa Ibom aka samu mutum 9, 7 a Rivers, 7 a Abuja, 6 a Bauchi, 5 a Osun kana da mutum 5 a jihar Oyo.

Shugaba Buhari yana nuna shaidar yin allurar riga-kafin covid-19
Shugaba Buhari yana nuna shaidar yin allurar riga-kafin covid-19

Sauran jihohin sun hada da 3 a Pilato, 3 Ekiti, 2 a Neja, 2 a Ogun da kuma mutum 1 a Zamfara.

Sai dai wannan adadi ya gaza wanda aka gani a ranar Juma’a, inda aka gano mutum 371 dauke da cutar, abin da ke nuna cewa adadin masu harbuwar na raguwa.

Hukumar ta NCDC ta ce ya zuwa ranar Asabar, ta sallami mutum 137, 645, amma adadin wadanda suka mutu kuma ya kai 1,964.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da Najeriya ta samu kayan allurar riga-kafin cutar ta COVID-19 miliyan 3.92 nau’in AstraZaneca a ranar Talata.

A ranar Asabar Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo suka yi allurar riga-kafin cutar, shirin da aka watsa shi kai-tsaye ta talbijin.

Shugaban Najeriya ya yi kira ga 'yan Najeriya da su rungumi allurar domin tana da fa'ida.

XS
SM
MD
LG